7 Yuli 2021 - 14:09
MDD Ta Yi Maraba Da Fara Rejistar Masu Zabe A Libya

Tawagar MDD dake kasar Libya (UNSMIL), ta yi maraba da kaddamar da aikin rejistar masu zabe wanda hukumar zaben kasar ta fara domin tinkarar zaben kasar dake tafe.

ABNA24 : UNSMIL ta taya hukumar zaben kasar Libya murnar kaddamar da aikin rejistar masu zaben, kuma tana daukar wannan mataki a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen tabbatar da burin da ake da shi na biyan muradun al’ummar kasar Libya don basu damar gudanar da babban zabe wanda aka shirya zai gudana a ranar 24 ga watan Disambar 2021.

A ranar Asabar, tawagar UNSMIL ta sanar cewa, taron jam’iyyun siyasar Libya, da aka shirya da nufin cimma matsaya ta karshe karkashin kundin tsarin mulkin kasar don daidaita batun zaben kasar dake tafe, ya ci tura bayan shafe kwanaki biyar ana tattaunawar a Geneva.

UNSMIL ta bukaci gamayyar jam’iyyun siyasar kasar LPDF, dasu gaggauta tattaunawarsu, domin cimma matsaya, kana su gabatar da bukatun game da zaben kasar bisa dacewa da kundin tsarin mulkin kasar.

342/